Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Boko Haram ta dauki alhakin harin Baga

Kungiyar Boko Haram ta ce ita ta kai harin nan na Baga da ke jihar Bornon Najeriya, a kwanan nan, inda ta hallaka daruruwan jamaa. Ta fadi hakan ne a cikin wani bidiyo da ta fitar a jiya. A halin da ake ciki kuma, gwamnatin Kamaru ta ce ta kwato Bajamushen nan da Boko Haram din ta sace a watan Yulin da ya gabata. Ga dai rahoton Abdullahi Kaura Abubakar daga Abuja: