Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An yi jana'izar Sarki Abdullah na Saudiyya

Ana zaman makoki a Saudiyya bayan mutuwar Sarki Abdullah Bin Abdulaziz. Ya rasu yana da shekaru tasa'in a duniya, bayan ya kwashe makonni a asibiti yana fama da ciwon hakarkari. Manyan shugabanni daga sassa da dama na duniya ne suka halarci jana'izarsa a ranar Juma'a. Sabon sarki Salman yayi alkawarin ci gaba da manufofinsa. Ga Isa Sanusi da rahoto a kan rayuwar marigayi Sarki Abdullah: