Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yaki da ta'addanci a kasashen yamma

Kasashen yammacin duniya na neman kwararan matakan magance tsatstsauran ra'ayi a gidajensu. Firaministan Australia ya ba da shawarar soke takardun zama dan kasa na wadanda aka samu da laifin ta'addanci, wadanda kuma ke da takardun zama 'yan wata kasar. A Faransa, hukumomi sun kwace fasfunan wasu 'yan kasar su shidda, wadanda ake zargi da shirin zuwa Syria don tallafa wa mayakan IS. A halin da ake ciki kuma, 'yan sandan Birtaniya sun je Turkiyya don nemo wasu dalibai mata su uku, wadanda ake jin suna shirin zuwa wajen mayakan IS a Syriar. Ga rahoton Aliyu Abdullahi Tanko: