Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Tallata 'yan takara a kafafen yada labarai

A Najeriya yayinda yantakara ke ci gaba da yakin neman zabe, kafofin yada labarai na taka muhimmiyar rawa a yakin neman zaben.

Sai dai kuma yayinda wasu ke ganin kafofin yada labaran na bai wa 'yan takara damar tallata kansu, wasu kuwa na ganin su na bari ana amfani da su don cin zarafin wasu 'yan takarar.

To shin menene ra'ayinku a kan wannan batun? Kuma ta yaya za a gyara? Wadannan na daga cikin batutuwan da zamu tattauna a filin Ra'ayi Riga na yau.