Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mun san inda Abubakar Shekau yake - Deby

Wasu da ake jin 'yan Boko Haram ne sun hallaka mutane fiye da sittin a garin Djaba na jahar Borno. Lamarin ya faru tun ranar Talata amma sai yanzu ake samun rahotanni. A cewar mazauna garin, maharan sun kashe maza, manya da matasa. A wani gefen kuma, a yakin da kasashe ke yi da 'yan Boko Haram din, shugaban Chadi ya ce sun san inda madugun kungiyar, Abubakar Shekau yake. Ga rahoton Isa Sanusi