Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 07/03/15

A Najeriya yayin da babban zaben kasar ke cigaba da karatowa 'yan gudun hijirar da ke zaune a garuruwan da ba sa cikin jahohin da hukumar zaben kasar ta ware domin gudanar da zabe na bayyana takaicinsu game da rashin damar da suke da ita ta yin zaben.

Ire-iren wadannan 'yan gudun hijira sun hada da wadanda ke Abuja, babban birnin Nigeriar, wadanda suka tsere daga garuruwansu sakamakon rikicin Boko Haram.

Hukumar zaben Najeriyar dai ta tsara cewa 'yan gudun hijirar da ke a jahohin Borno da Yobe da Adamawa ne kadai keda damar kada kuri'a.

Ibrahim Mijinyawa ya zanta da wasu 'yan gudun hijirar dake zaune a Abuja; ga kuma rahoto na musamman da ya hada mana: