Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Amfani da na'urar 'Card Reader' a zaben Nigeria

A ranar Asabar da ta wuce ne hukumar zabe ta kasa a Nigeria, INEC ta gudanar da gwajin amfani da na'ura mai kwakwalwa ta Card Reader, wajen tantance sahihancin katin rajistar masu kada kuri'a a lokacin zabe. Hukumar zaben dai ta ce ta dauki wannan mataki ne domin kawar da shakkun da wasu suke da shi game da ko na'urar za ta yi aiki ko akasin haka. An yi wannan gwaji ne a jihohi goma sha biyu, a sassa daban daban na Nigeriar. Sai dai bisa dukkan alamu an samu rarrabuwar kawuna game da aiki da wannan kati na didindin a lokacin zabukan dake tafe. Yayinda Jam'iyyar PDP mai mulki ke nuna adawa da shi, jam'iyyar adawa ta APC na cewa tana goyon bayan aiki da shi. Shirin Ra'ayi Riga na yau zai yi nazari ne kan yadda gwajin ya kasance, da irin nasarorin da aka samu,da kuma matsalolin da aka fuskanta a aikin.