Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 05/04/2015

Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da jinjina wa Nijeriya kan yadda ta shirya zaben shugaban kasa da ake yi wa kallon mai inganci, inda shugaban dake kan karagar mulki ya fadi zabe, ya kuma rungumi kaddara, wata kasa da ta taba samun kanta a irin wannan matsayi ita ce kasar Ghana.

A kasar ta Ghana dai jam'iyyar dake mulki ta fadi zabe, lamarin da ya sa shugaban Amurka Barack Obama ya jinjina ma kasar har ya kai ma ta ziyara.

To daga wancan lokaci zuwa yanzu ko wane irin amfani Ghanar ta samu, kuma wane amfani Nijeriya zata iya samu daga wannan matsayi da ta samu kan ta a ciki yanzu?

Wakilinmu Iddi Alli a birnin Accra ya shirya mana wata tattaunawa ta musamman kan wannan batu, da wasu malamai da ya gayyata;