Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda ake yaudarar mata su shiga karuwanci - Kashi na 2

Kusan mata da 'yan mata 800 ne aka tilastawa yin karuwanci a bara, kamar yadda hukumar da ke kula da laifuka ta Biritaniya ta bayyana. Masu safarar mutane ne ke da alhakin wannan aika-aikar. Wasu kungiyoyi da ke aiki tare da mutanen da aka jefa su cikin wannan yanayin, ciki har da kungiyar Poppy Project sun ce lamarin na kara muni. Ope mai shekaru 24, ta ce a shekara ta 2005 ta hadu da wani mutumi wanda ya yaudare ta zuwa Turai a kan cewa zai samar ma ta da aikin yi me kyau. Sashin Hausa na BBC ya soma ba da labarin Ope kuma wannan shi ne kashi na uku kuma na karshe.

An sauya sunan Ope domin a kare ta.

@jim_reed ne ya yi hirar sannan Jesse Brown.