Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mahimmancin kada ganga a Burundi

Kada gangunan gargajiya a Burundi dai, wani batu ne da 'yan kasar ke alfahari da shi matuka.

Hakan ya sa har Hukumar kula da ilimi da kimiya da kuma al'adun ta majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta ba kidan wani matsayi na musamman. Kidan ya yi fice ne ba kawai saboda sautinsa ba, har ma da raye-rayen da ake yi da shi.

Yanzu makadan sun yi kiran da aka sa tsari a harkar. Ga dai rahoton Jimeh Saleh