Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 18/04/2015

A karshen makon jiya ne aka gudanar da zabukan gwamnoni da yan majalisun jihohi a Nigeria, zaben da ya zo makwanni biyu dai-dai bayan gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majlisun dokoki na tarayya, wanda Janar Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa bayan lashe zaben.

A wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shugaban mai jiran gado, Janar Buhari ya ce ya yi mamaki da irin sauyin da aka fara gani a Nigeria daga lokacin da aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe.

An yi wannan hira a ranar da aka gudanar da zaben na gwamnoni, kuma tambayar farko da Yusuf Ibrahim Yakasai ya yi wa shugaban mai jiran gado ita ce ta yadda yake kallon zaben na gwamnoni.