Gane Mani Hanya 25/04/2015

Matashin nan dan Najeriya, Sulaiman Hashimu mai shekaru 33 wanda ya yi tattaki daga Lagos zuwa Abuja ya ce ya ga abubuwa da dama daga cikin matsalolin da 'yan Najeriya ke fuskanta a rayuwa ta yau da kullum.

Shi dai wannan matashi ya yi wannan tafiyar ce domin cika al'kawarin da ya yi cewa, idan Janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasa zai yi wannan tattaki a kas.

A hirarsu da Abdou Halilou, ya warware zare da abawa kan irin abubuwan da ya fuskanta akan hanya. Ku saurari yadda hirar tasu ta kasance: