Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dan Nigeria da ya tsallaka bahar rum

Daruruwan 'yan ci-rani na tsallaka tekun Bahar Rum a kowacce rana, domin shiga kasashen Turai, musamman Italiya da Girka. Yawancin su su kan isa bakin tekun da kayayyakinsu da kudade. Amma da yawa su kan rasa komai a lokacin da ake tafiya a tekun. Kingsley dan Najeriya, yana daya daga cikinsu; ya sami kansa da kwana a tsibirin Leros na Girka, har zuwa lokacin daya sami kudi sannan ya ci gaba da balaguron. Ya shaida wa wakilin BBC Murad Shishani labarinsa.