Rikicin Burundi
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Dambaruwar siyasar Burundi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kasar Burundi ta yi fama da rikicin nuna adawa da ta-zarce.

Al'umar Burundi ta samu kanta cikin yamutsi da kuma rashin tabbas game da makomar mulkin demokuradiyya a kasar.

Tun lokacin da shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta yin ta-zarce wasu 'yan kasar suka shiga zanga-zangar kyamar wannan yunkuri, yayin da wani bangaren sojin kasar yayi ikirarin kifar da gwamnatin shugaba Nkurunziza, daga nan kasar ta shiga rudani!

Gwamnatin kasar tace ta karya lagon masu juyin mulkin kuma ta kame wasu daga cikinsu.

Ta yaya za a warware matsalar Burundin da kuma tazarce dake neman zama annoba a nahiyar Afrika.

Kadan kenan daga cikin batutuwan da shirin Ra'ayi Riga ya tattauna a kai.