Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 16/05/2015

A Najeriya yayin da ya rage kasa da makonni biyu a mika mulki ga sabuwar gwamnati, bisa ga dukkan alamu ana cin karo da wasu matsaloli a wajen samar da bayanai daga gwamnati mai barin gado zuwa gwamnati mai shigowa.

Alhaji Dikko Umar Radda, shi ne sakataren harkokin walwala na kasa na jam'iyyar APC, kuma yayin wata ziyara da ya kawo sashen Hausa na BBC a farkon makon da ya gabata, ya tattauna da Ahmad Abba Abdullahi game da shirye shiryen jam'iyyarsu na kafa gwamnati;

Ga yadda hirar tasu ta kasance.