Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shan miyagun kwayoyi:Kashi na 2

To yanzu sai kashi na biyu na rahoton da muka kawo maku a jiya, kan matsalar fataucin miyagun kwayoyi a Guinea-Bissau. Kasar dai ta zama wurin yada zango na masu fataucin miyagun kwayoyin daga yankin kudancin Amirka zuwa Turai. Za mu kara jin labarin Buba, wani matashi mazaunin Bissau, babban birnin kasar ta yammacin Afirka. An sauya sunayen mutanen da za ku gani a zanen. Kuma akwai wasu batutuwan da ba su dace da kananan yara ba. Ga rahoton Isa Sanusi: