Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 23/05/2015

A cikin makon da ya gabata ne shugaban jam'iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu, da kuma shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar, Chief Tony Anenih, suka yi murabus daga mukamansu.

Murabus din ya biyo bayan kayen da jam''iyyar ta sha ne a zabukan da aka gudanar a Nijeriya a watannin Maris da Afirilu, inda a karon farko a tarihin Nijeriya aka kayar da shugaban kasa mai ci a zabe, bayan da dan takarar jam'iyyar APC Muhammadu Buhari ya samu nasara kan shugaba Goodluck Jonathan.

Shin menene ya sa shugabannin jam'iyyar PDP kan rasa mukamansu cikin yanayi na takaddama? Kuma Ina makomar jam'iyyar PDP a siyasar Nijeriyar?

A filinmu na Gane Mani Hanya, Wakilinmu Is'haq Khalid ya duba mana wannan batu ga kuma rahoto na musamman da ya aiko mana daga Bauchi.