Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ta yaya Buhari zai yaki cin hanci da rashawa ?

A lokacin yakin neman zabensa, shugaban Najeriya mai jiran gado Muhammadu Buhari ya ce, idan aka zabe shi, zai maida hankali kan magance wasu matsaloli uku da ke addabar kasar.

Sun hada da rashin tsaro, da rashin aikin-yi da kuma cin-hanci da rashawa. To a kan haka ne zamu kawo mu ku jerin rahotanni kan kowace daga cikin wadannan matsaloli.

Wakilinmu a Abuja, Haruna Shehu Tangaza ya duba batun cin-hanci da rashawa, ga kuma rahotonsa.