Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari

An yi bikin rantsar da sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a Dandalin Eagle Square da ke birnin Abuja.

Ranar na cike da tarihi a Najeriya, inda a karon farko tun bayan komawar kasar bisa tafarkin dimokradiyya a 1999, mulki ya koma hannun wata jam'iyyar adawa.

A jawabinsa a wurin bikin, Muhammadu Buhari ya yi alkawarin bunkasa wadata a Najeriya.

Ga dai rahoton Editanmu Mansur Liman daga Abuja: