Dakarun Nigeria na cin zarafin bil'adama

Kungiyar Amnesty International ta zargi wasu kwamandojin sojan Najeriya da alhakin mutuwar dubban matasa maza, wadanda suka tsare.

A rahoton da ta fitar kan yaki da Boko Haram, Amnestyn ta ce, ya kamata a binciki jami'an sojan game da aikata laifukan yaki, da kuma laifuka a kan bil'adama.

Amnesty din ta zargi su ma 'yan Boko Haram da irin wadannan laifufuka.

Wannan rahoton na Isa Sanusi na dauke da hotunan da watakila za su ta da maku hankali: