Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya

Matsalar tsaro a sashen arewa maso gabashin Nigeria,musamman yaki da 'yan Boko Haram, matsala ce da aka yi ta daukar matakai iri daban daban a yunkurin ganin bayanta.

Duk da shekarun da aka kwashe ana yaki da wadannan masu tayar da kayar baya, kusan dai har ya zuwa yanzu lamarin sai kwan-gaba kwan baya ake yi.

Rikicin Boko Haram dai ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane da lalata dukiyoyi masu dimbin yawa. A kwanakin baya ne wasu 'yan asalin Jihar Borno, Barrister Zanna Mustapha, da Muhammad Bolori suka kawo mana ziyara a sashen Hausa na BBC, Ahmad Abba Abdullahi ya tattauna da su kan yadda suke gani ya kamata a tunkari matsalar. Farko ga Barrister Zanna Mustapha.