bukola saraki
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Dambarwar shugabanci a majalisa

Zaben shugabannin majalisun dokokin Najeriya ya bar baya da kura, tun da ya jefa majalisun da 'ya'yansu cikin wata dambarwar da har kansu ya rabu. Jam'iyyar APC mai mulki na jin takaicin shugabancin ya kauce ma wadanda take goya ma baya, yayin da Jam'iyyar adawa ta PDP ke madallah da zaben.

Shin yaya wannan dabarwar za ta shafi harkokin mulki a Najeriya a cikin shekaru hudun da ke tafe?

Kuma mene ne ya hada jam'iyyar APC da 'ya'yanta har aka samu wannan baraka?

Kadan kenan daga cikin batutuwan da za mu tattauna a filin ra'ayin riga na wannan makon.