Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 13/06/15

A kwanaki ne hukumar hana fasa kauri ta Nigeria ta kama wasu kayayyaki a Kano wadanda tace an shiga da su kasar ne ta haramtacciyar hanya.

Hukumar ta Custom ta kama kayan ne a wasu manyan dakunan ajiye kaya, wadanda mafi yawansu atamfofi ne da aka hana shiga da su Nigeria.

Hukumar ta yi zargin cewa wasu 'yan kasar China ne suka shiga da haramtattun kayan Nigeria, ta harmatacciyar hanya.

To sai dai tun bayan kame kayan, 'yan kasuwar kantin kwari na cewa al'amurra sun tsaya cak a kasuwar, a dai dai lokacin da yafi kowane hada hada a shekara.

Yau a filinmu na Gane Mini Hanya wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya duba mana wannan batu, ga kuma rahoto na musamman da ya hada mana: