Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugaba al-Bashir ya koma Khartoum

Shugaban Sudan, Omar al-Bashir ya koma gida daga Afirka ta kudu, bayan yayi biris da wani yunkuri na mika shi ga kotun duniya, bisa zargin aikata kisan kare dangi.

Al Bashir, wanda ya halarci taron kolin Tarayyar Afirka, ya yi watsi da wani umurnin kotu na neman ya tsaya a Afirka ta Kudun.

Ba a san ko za a hukunta Afirka ta Kudun ba, saboda ta bar shi ya sulale.

Ga rahoton Abdullahi Tanko Bala.