Jirgi marar matuki na farinjini a Amurka

Amerikawa sun gano hanyoyi da dama na amfani da jiragen nan marasa matuka, watau drones. Jama'a da dama dai na ganin cewa zaa iya samun alheri a wannan harka da kasuwarta ta kai miliyoyin daloli. Hakan ya sa Hukumar sufurin jiragen sama ta Amurka na kokarin bullo da wani tsari domin 'yan kasuwa da masu nishadi su rika amfani da irin wadannan na'urori. Ga dai Isa Sanusi da karin bayani: