Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An kori marasa galihu a wani yankin Accra

'Yan sanda a Ghana sun harba borkonon tsohuwa domin tarwatsa dubban jamaa da ke zanga-zangar nuna adawa da rusa gidaje a wata unguwar marasa galihu da ke Accra. Mutane fiye da dubu 50 ne dai ke zaune a unguwar da ake kira Sodom da Gomorrah. Mahukunta dai sun ce gine-ginen unguwar sun toshe magudanan ruwa, abun da ke haddasa ambaliyar ruwa wadda ta hallaka mutane dari da 50 a farkon wannan watan. Ga dai rahoton Aminu Abdulkadir