Gane Mini Hanya 27/06/2015

Gwamnatocin kananan hukumomi su ne ake cewa mafi kusa da jama'a. Sai dai a Nigeria kananan hukumomin sun samu kansu a tsaka mai wuya, a 'yan shekarun nan, kama daga batun asusun hadin gwiwa zuwa abin da ya shafi baiwa kananan hukumomin ikon cin gashin kai.

Kwanakin baya da shugaban kungiyar Ma'aikatan kananan hukumomi ta Kasa a Nigeria,NULGE, Comrade Ibrahim Khalil ya kawo mana ziyara, Ahmad Abba Abdullahi ya tattauna da shi kan batutuwa da dama. Ya fara ne da batun samun sabuwar gwamnati a Nigeriar.