Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Me kuka sani game da Tsibirin Goree?

Tsibirin Goree na gabar ruwan Senegal, ya kasance cibiyar cinikin bayi mafi girma a gabar Afirka.

Daga karni na goma sha biyar zuwa sha tara an kiyasta cewa, 'yan Afirka miliyan ashirin ne suka bi ta wurin.

A yanzu dimbin jama'a ne ke zuwa tsibirin na Goree domin shaida abinda ya faru a tarihi.

Wakilinmu Haruna Tangaza, ya sami zuwa tsibirin a kwanan nan, ga kuma tsarabar da ya kawo mana: