Gane Mani Hanya 04/07/15

Gane Mani Hanya 04/07/15

Ma'abota wasannin motsa jiki na cigaba da nuna azama duk da Azumin Ramadan da ba kasafai jama'a kan kasance da karsashi ba. An cigaba da gudanar da wasanni da suka kama daga kwallon kafa da kwallon kwando dana tennis da kuma guje guje da tsalle tsalle da sauransu.

Sai dai masu yin wasannin gargajiya da ya hada da Dambe da kokawa da langa sun tafi hutu sai bayan an kammala azumi wato bayan bikin sallah kenan.

Ga rahoton da Muhammad Abdu Mam'man Skeeper ya hada mana.