Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Obama ya gargadi mahukuntan Habasha

Shugaba Obama ya gargadi mahukuntan Habasha da cewa, ya kamata su kyautata batun kare hakkin bil'adama da kuma mulki nagari a kasar.

A ziyarar da ya kai a birnin Addis Ababa, mista Obama ya ce, yayi tattaunawar keke da keke da Praministan Habashar.

Ya ce kasar zata yi karko idan kowa ya sami izinin fadin albarkacin bakinsa. Ga Isa Sanusi da karin bayyani: