Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An yanke wa Saif al Islam Gaddafi hukuncin kisa

Wata kotu a Libya ta yanke hukuncin kisa a kan dan gidan marigayi Moammar Gaddafi, Saif al Islam da wasu mutane takwas.

Wasu daga cikin mutane takwas din da kotun ta yanke wa hukuncin kisa su ne Abdallah al-Senousi, tsohon shugaban hukumar leken asiri da Al-Baghdadi al-Mahmudi, tsohon Firai Mininstan kasar.

Ga Abdullahi Tanko Bala da karin bayani.