Wayoyin hannu sun doke komfuta

Computer Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Komfutar tafi da gidanka ta dauko hanyar zama tsahon yayi a sanadiyyar burinkasar wayoyin hannu na zamani da ake shiga yanar gizo da so cikin sauri da kuma daukar hotuna masu kyau

A karon farko wayoyin hannu na zamani sun zarce na'urar komfutar tafi da gidanka a matsayin abubuwan da mutanen Birtaniya suka fi so wajen shiga yanar gizo.

Wannan sakamakon wani bincike ne da wani kamfani Ofcom ya gudanar a kasar, a inda ya nuna cewa kashi 33 na 'yan kasar sun fi son wayoyin hannun a shekarar 2014 fiye da kashi 30 wadanda su ka fi son amfani da komfutar tafi da gidanka watau laptop.

Bayannan binciken ya nuna cewa turawan Ingilan sun dauki hoton kansu da kansu watau selfie sau miliyan 1 da milyan 2 a shekarar da ta wuce.

A kalla magidanci 1 a cikin magidanta 10 ne ya dauki kan sa hoto a kalla sau 1 a mako, in ji binciken na Ofcom.

Yawan samun wayoyin na zamani masu daukar kyawawan hotuna na daya daga cikin dalilian da suka habbaka sayen wayoyin in ji binciken