Lambobin kulle komfuta sun soma rauni

Komfuta Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Da lambobi ne ake tsara fasahar kulle komfuta a inda suke fitowa a hargitse ta yadda zai wahala ga barawo ya yi satar bayanai.

Fasahar da ake amfani da ita wajen kulle miliyoyin bayanai a cikin rumbunan tara bayanai ga masu amfanin yanar gizo na kara yin rauni in ji wani bincike.

Binciken ya gano cewa yawan adadin lambobin masu wuyar ganewa da ake samar da su domin kulle rumbunan bayanan suna da muhimmanci don gujewa kutse cikin naurorin domin sata.

Masu binciken sun yi gargadin samun rauni ga wanda hakan zai sa a iya kutse cikinsu kuma sace bayanan.

kwarraru akan fasahar tsaro na na'urar mai kwakwalwa Bruce Potter da Sasha Moore wadanda suka yi bincike sun ce abin da na tayar da hankali.