An raunata tsaron fasahar Android

waya
Image caption Wayar hannu samfurin android masu farin jini na amfani da fasahar tsaro na ASLR wanda bincike ya gano cewa yana da matsala ta fuskar tsaro

Wata fasahar da aka kirkiro domin magance matsalar tsaro a wayoyi samfurin android na da matsala.

Matsalar tsaron da aka gano sun shafi wayoyin hannu na android kimanin biliyan daya a cewar masu binciken manhaja.

Kamfanin Google ya samar da wata fasahar maganin matsalar amma wani kamfanin tsaro na fasahar ya raunata abinda da suka yi. Ya kuma kara da da cewa fasahar tsaron na jeka na yi ka ne kawai.

Kamfanin Google ya yiwa BBC bayanin cewa akasarin wayoyin hannu samfurin android na amfani ne da fasahar tsaro na ASLR wanda ke cikin kimanin kashi 90 na wayoyin.

Fasahar ASLR na dakile yiwuwar yin kutse cikin wayar da ke dauke da ita.