Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Harin bam a Bangkok

'Yan sanda a Thailand sun ce akalla mutane 19 ne aka kashe a wani harin bam a kan wani wurin ibadar mabiya addinin Hindu a birnin Bangkok. Wasu karin mutanen fiye da dari da 20 kuma sun jikkata. Rahotanni sun ce an kai harin ne a kan babur, kuma yankin na da cunkoson jamaa. Ga dai Aminu Abdulkadir da karin bayani: