Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hira da Sani Danja kan sabuwar wakarsa

Masu mu'amala da shafin sada zumunta na Twitter sun yi tsokaci sosai a kan wata sabuwar wakar da jarumin fina finan Hausa, Sani Danja ke shirin kaddamarwa.

Wakar, mai suna As E Dey Do Me a turance, ta dauki hankali ma'abota shafin sada zumuntar ne saboda an yi amfani da harshen Hausa da Turanci a cikinta.

Sani Danja ya shaidawa BBC cewa wakar ta yi masa bazata, yana mai cewa bai yi tsammaci za ta ja hankalin jama'a haka ba, kamar yadda ya fadi a hirarsa da Badariyya Tijjani Kalarawi.