Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 29/08/2015

Tuni maniyyata aikin hajjin bana daga dukkan kasashen musulmi suka fara isa kasar Saudi Arabia domin fara aikin hajjin, wanda daya ne daga cikin shika- shikan musulunici guda biyar.

A nahiyar Afrika, Najeriya na daga cikin kasashen da suka fi yawan masu zuwa aikin hajji a duk shekara.

A duk shekara dai a kan samu korafe- korafe daga alhazan kan irin damfara da ake yi musu a lokacin aikin hajjin, tun daga gida har zuwa kasar Saudiya.

A filin Gane Mini Hanya na wannan mako, wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai ya duba mana wasu daga matsalolin da alhazai ke fuskanta a lokacin aikin hajjin da kuma matakan da ake dauka dan magance wadannan matsalolin.