Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hira da Buhari kan kwanakinsa 100 a kan mulki

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce jami'an tsaron kasarsa sun samu nasara matuka a yaki da kungiyar Boko Haram.

A hirarsa da Editan sashen Hausa na BBC, Mansur Liman, shugaba Buhari ya ce akwai bukatar a kara matsa kaimi wajen kawo karshen 'yan kunar bakin wake wadanda ke ci gaba da kaddamar da hare-hare.

Mansur Liman din ya fara ne da tambayarsa ko a ina aka kwana a yaki da kungiyar Boko Haram?