Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kashi na biyu na hira da Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce yana samun hadin kan kasashen duniya domin kwato kudaden da aka sace musamman na danyen mai da ake sacewa a cikin teku. A kashi na biyu na hirarsa da BBC, albarkacin cikarsa kwanaki dari a kan karagar mulki, shugaba Buharin ya ce nan ba da jimawa ba za a fara gurfanar da wadanda ake zargi a gaban sharia. Ga dai karin bayanin da ya yiwa Editan sashen Hausa, Mansur Liman.