Gungun mahara ya matsawa kamfanoni a intanet

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An amfani da bitcoin wajen saye da sayarwa a intanet

Wani gungun mahara masu kwace ta intanet ya sa Bankuna da kafofin yada labarai da kamfanonin kera manhajar wasanni a gaba.

Gungun ya sa su a gaba ne ta hanyar yi musu barazar su biya su wasu kudadade ko su lalata shafukan na kasuwancinsu na intanet.

A cikin wani rahoto da Akamai wani kamfanin intanet ya fitar, ya ce a watanni 10 da suka wuce gungun ya kai wa masu ciniki da su hari har sau 141 a intanet

Gungun maharar ta intanet da ake kira DD4BC ya yi barazanar makare rumbun ajiyar bayanan kamfanin idan bai biya fansar kudin intanet bitcoin 50 kimanin £8,000 ba.

Gungun na kai hari a shafukan intanet ta hanyar cika shafin wanda ya ke hari da ambaliyar gigabits 56 na bayanai a dakika 1.

A cewar rahoton Akamai gungun maharan na DD4BC na nan tun cikin watan Satumba na 2014 sai dai a kwanakin nan ne ya matsa kaimi da kai hari akan harkokin kasuwanci a intanet.

Harkokin hada-hadar kudi na daya daga cikin inda gungun ya matsawa lamba ta hanyar kwace da cin zarafi da batanci da kuma sa a ji kunya a idon jama'a a cewar Stuart Scholly shugaban tsaro na kamfanin Akamai.