Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 19/09/2015

A Jamhuriyar Nijer, wasu masu shirya fina-finai 'yan Najeriya da 'yan Nijer sun kammala matakin farko na shirya wani shirin fim da za a rika yi daki-daki, wato 'Series', mai suna 'Warisha'.

Fim din dai ya mayar da hankali ne a kan matsalolin rayuwa kamar karuwanci, da shaye-shaye, da kuma irin halin da matasan Afirka ta Yamma kan tsinci kansu a ciki idan suka bar gida.

An dai shirya fassara jerin shirin fim din zuwa harsunan Faransanci, da Ingilishi, da kuma harshen Swahili domin a rika nuna shi a gidajen talabijin na kasahen Afirka.

A filin Gane Mini Hanya na wannan makon wakilinmu BARO ARZIKA a Yamai ya tattauna da wasu 'yan wasan da kuma masu jagorancin shirin na 'Warisha'

Ya soma tattaunawar da Malam Mika'il Isa ibn Hassan wanda aka fi sani da sunan Gidigo: