Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Za a yi ruwan sama mai karfi a gabashin Afrika

Ana sa ran a kowane lokaci daga yanzu za'a tafka ruwan sama da baa taba ganin yawansa ba a cikin fiye da shekaru 30 a Gabashin Afrika. Musabbabin al'ammarin dai, shi ne sauyin yanayi inda ruwan teku ke yin zafi fiye da kima. Yanzu haka dai jamaa na kimtsawa domin takaita asarar rayika da ta dukiyoyi. BBC ta leka kudancin Kenya don ganin halin da ake ciki. Ga dai rahoton Jimeh Saleh.