Mutane sun fi son Butum butumi mai dabi'u

Image caption Butum butumi mai dabi'a tamkar ta mutum.

Butum butumi da su ke nuna wasu nakasu irin ta dan adam za su fi saurin samun karbuwa wurin mutane fiye da wadanda ba su da nakasu shi, a cewar masu bincike.

Wasu kwarraru daga jami'ar Lincoln sun gano cewa mutane sun fi son butum butumin da ke yin kurakurai ya ke kuma yin wadansu dabi'u irin na dan adam kamar gundura ko rashin nishadi

Domin aikin gwaje-gwajen butum butumin an tsara su da su rika yin kurakurai a ya yin da ake lura da mutane da ke wurin kuma ake gwajin da su.

Sakamakon binciken ka iya sauya yadda kirar butum butumin za ta kasance, in ji masu binciken.

Dokta John Murray na jami'ar Lincoln sashen ilimin komfuta da kuma mai binciken digirin dokta Mriganka Biswas ya gudanar da gwaje-gwaje da wasu butum butumi guda 3.

Butum-butumi na farko shi ne Erwin (mai kamanceceniyar dabi'u irin na bil adama) wanda sashen nazarin ilimin na'ura mai kwakwalwa na jami'ar Linclon ya kera, zai iya kuka da dariya da bakin ciki da kuma farin ciki.

Na biyun kuma mai suna Keepon, wani dan karamin butum butumi ne wanda aka kera shi domin ya yi nazarin cigaban alumma ta hanyar mu amilla da yara.

Na ukun kuwa kera shi aka yi ta hanyar fasahar zamani da aka sa wa suna Marc.

Masu binciken sun gudanar da wasu jerin gwaje-gwaje wadanda su ka hada da butum butumin yin wasu kurakurai da rashin fahimta da kuma dabi'u irin na bil adama kamar gajiya da gundura da kuma farin ciki.

Kuma cikin rabin lokacin da su ke mu'amilla da mutane wadan nan dabi'un ga butum butumin ko a jikinsu.

Mun lura da mutanen da muke gwajin a kansu ta yadda suke ji game da butum butumin, mun kuma gano cewa sun rike hankalinsu na tsawon lokaci kuma sun ji dadi ganin cewa butum butumi na iya yin kuskure da manta bayanai ya kuma nuna wasu dabi'u irin na kamar farin ciki tamkar dan adam, a cewar Mista Biswas