Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kiwon jimina a Afrika Kudu

Shekaru hudu da suka wuce, masu kiwon jimna a Afrika ta Kudu sun shiga wani mawuyacin hali, sakamakon bullar cutar murar tsintsaye da kuma haramcin da Tarayyar Turai ta saka na shigowa da danyen naman jimna cikin kasashen kungiyar. Jimna kusan dubu 50 ne aka kashe domin hana yaduwar cutar, kuma dubban ma'aikata sun rasa ayyukansu. Sai dai yanzu kiwon jimnar na farfadowa . Ga rahoton Abdullahi Tanko Bala.