alassane_ouattara
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ouattara ya yi tazarce a Ivory Coast

Shugaba Allasane Ouattara na Ivory Coast ya lashe zaben da aka yi a ranar Lahadi da ta gabata da gagarumin rinjaye. Ya samu kusan kashi 84 cikin 100 na kuru'un da aka kada. Babban abokin hammayarsa na jam'iyyar FPI, Pascal Affi N'Guessan ya samu kashi 9 ne cikin 100 na kuru'un. Wasu 'yan takarar adawa dai sun yi kiran a kauracewa zaben, suna masu cewa akwai wani shiri na tafka magudi. Sai dai a ranar Litinin masu sa ido a zaben daga Amurka, sun ce zaben sahihi ne. Ga dai Aichatou Moussa da karin bayani: