Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ministoci marasa ma'aikatu a Nigeria

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce cikin ministocin da za a nada za a samu wadanda ba lalle ne a ba su rikon wata ma'aikata ba. Ya dangana hakan ga karancin kudi da kasar ke fama da shi. Yaya girman wannan matsala take, kuma yaya za a shawo kanta. Wadannan suna cikin batutuwan da za mu tattauna a wannan makon, a filinmu na Ra'ayi Riga.