Yaya daidaito tsakanin maza da mata yake?

Idan kuka yi nazari kan wannan taswirar ta BBC, za ku ga bambancin da ke tsakanin maza da mata a kasarku, da kuma matsayin ta a kan batun a duniya.

Ka sanya sunan kasarka a cikin "akwatun bincike" domin ganin matsayin kasarka kan daidaito tsakanin maza da mata. An samu alkaluman bambance-bambance tsakanin maza da mata ne daga rahoton taron tattalin arziki na duniya wanda ke auna matsayin kasashe kan yadda mata ke shiga a dama da su a harkokin siyasa da tattalin arziki da ilimi da lafiya.

An samu rahoton daga:

Taron tattalin arziki na duniya, da cibiyar kididdiga ta Unesco.

Tsari

Ta lokacin da yake nazari kan bambance-bambance tsakanin maza da mata, taron tattalin arziki na duniya ya duba hanyoyi da dama a kan shiga harkokin tattalin arziki da samun dama, da samun ilimi da kiwon lafiya da harkokin siyasa.

An auna matakin da kowacce kasa take a kan daidaito tsakanin maza da mata bayan da aka yi la'akari da irin damar da kowacce kasa take bai wa mutane. Hakan ya sa aka ware kasashen da suka fi arziki da wadanda suka fi talauci.

Rahoton da aka fitar a bana shi ne karo na goma da taron tattalin arzikin ya fitar, inda ya yi nazari a kan kasashe 145.

An samu bayanai kan bambancin da ke tsakanin maza da mata ne daga kungiyar hada kai domin bunkasa tattalin arziki da ci gaba (OECD). Haka kuma alkaluman da aka samu su ne na baya bayan nan kan kowacce kasa daga shekarar 2010-13.

Kungiyar OECD ta duba bambancin da ke tsakanin maza da mata ta hanyar kudin da kowannesu ke samu. Kuma an yi lissafi ne kan wadanda ke yin cikakken aiki.

Haka kuma an samu alkaluma kan adadin matan da suka gama Jami'a ne daga wajen cibiyar kididdiga ta Unesco.