Yadda
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bayelsa: Ana tattara sakamakon zabe

Yanzu haka ana ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan da aka yi jiya a jihar Bayelsa ta kudu maso kudancin Nigeria.

Fafatawa a zaben dai ta fi zafi ne tsakanin gwamna mai ci, Henry Seriake Dickson na jam'iyyar PDP da kuma Timipre Sylva na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

An bada rahotannin samun tashin hankali a wasu sassa, kuma tuni hukumar zabe INEC ta sanar da cewa, za a sake zabe nan gaba a karamar hukumar Southern Ijaw.

Jihar Bayelsa na daga cikin jihohin Nigeria a dake da dimbin arzikin mai.

Tun daga lokacin da aka kafa jihar jam'iyyar PDP ce take mulki.