Za a kirkiro fasahar gano kalaman batanci a intanet

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban kamfanin Google Mista Schmidt

An yi kira ga kamfanonin fasaha da su samar da fasahar da za ta dakile ayyukan ta'addanci ta hanyar kirkiro manhajjar da za ta gano kalaman batanci a shafukan sada zumunta da muhawara.

Shugaban kamfanin Google Eric Schmidt ne yayi wannan kira a wata makala da ya rubuta a jaridar New York Times.

Mista Schmidt ya ce a samar da fasahar wacce da kanta za ta tsamo kalamai masu nasaba da tsattsauran ra'ayi da kuma wacce za ta cire hotunan bidiyo a dandalin sada zumunta da muhawara kafin a yada su.

Mista Schmidt ya ce fasahohin za su taimaka wajen kwantar da hankali a shafukan intanet.

Makalar ta Mista Schmidt ta zo daidai lokacin da Hillary Clinton 'yar takarar shugaban kasa a jam'iyyar Democrat a Amurka ta sake yin kira ga masu kirkiro manhajojin komfuta na kasar da su taimaka a yaki ta'addanci musamman ta hanyar samar da fasahar da za a yaki kungiyar IS da ita.

Gwamnatoci da kamfanoni sun yi ta kokawa da juna kan yadda za a tunkari barazanar ta'addanci bayan harin da aka kai birnin Paris.

A yayin da muhawara a kan ta'addanci ta zafafa bayan harin da aka kai San Bernardino, makalar da Mista Schmidt ya rubuta, wani yunkuri ne na kwantar da hankali da kuma nuna aniyar kamfanonin na bayar da ta su gudunmawar.