Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tela makaho a kasar Tanzania

'Yan magana dai sun ce kowa da baiwar da Allah ya ba shi. Wannan dan Tanzaniar mai suna Abdallah Nyangalio, makaho ne, kuma tela. Bugo da kari, wadanda yake yi wa dinkin, sun hada da tsohon shugaban kasa, Jakaya Kikwete da kuma Anna Mkapa, matar tsohon shugaban kasar, Benjamin Mkapa. To BBC ta gaana da Abdallah Nyangalion, domin jin karin bayani a kan rayuwarsa: